1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An Soki sabon tsarin Amirka

November 5, 2010

Ƙasashen dake da ƙarfin tattalin arziki a duniya, sun soki shirin zaburar da tattalin arzikin, wanda ƙasar Amirka ta fitar

https://p.dw.com/p/Q0BZ
Ministan kuɗin Jamus Wolfgang SchaeubleHoto: AP

Ƙasar Jamus da China sun suke sabon shirin zaburar da tattalin ariki, wanda gwamnatin ƙasar Amirka ta fitar. Ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble, yace yana ganin wannan tsarin da Amirka ta fitar na zuba dala biliyan 600 don zaburar da tattalin arzikin ta, dakuma rage kuɗin ruwa, a matsayin wata gurguwar dabara. Schäuble yace da alamu Amirka so take ta karya dajarar dala, kan sauran kuɗaɗen ƙetare. Shi ma muƙaddashin ministan harkokin wajen China, yace baya maraba da shirin da baitil malin Amirka ya fitar. Wannan matakin dai zai ƙara ruruta taƙaddamar da ake yi kan darajar kuɗin duniya, gabanin taron ƙungiyar ƙasashe ashiri mafiya ƙarfin tattalin arziki a duniya wato G20, da zai gudana a Koriya ta kudu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala