1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma yin jana'izar Muhammad Ali

Abdourahamane HassaneJune 9, 2016

Za a yi kwanaki biyu ana yin jana'izar shahararan tsohon dan wasannin daben boxe ɗin nan,Muhammad Ali a garin Louisville na Amirka inda nan ne mahaifarsa

https://p.dw.com/p/1J3RL
USA Kollektive Trauer um Muhammad Ali in Louisville
Hoto: Reuters/John Sommers II

Sama da 'yan jaridu dubu biyu ne da masu ɗaukar hoto daga ƙasashen duniya za su halarci wannan jana'iza da za a yi yau Alhamis da gobe Jumma'a.Tare da halarta wasu daga cikin shugabanin ƙasashe a ciki har'da na Turkiyya Recep Tayib Erdogan.

Shugaba Barack Obama ba zai samu damar halarta jana'izarba saboda wani uzirin da ke gareshi sai dai zai tura wakili.Muhammad Ali ya rasu a ranar Jumma'a da ta gabata yana da shekaru 74,kuma tun daga shekara ta 1984 ya fara jinya cutar zanzzanar jiki watau Parkison