1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sulhunta makiyaya da manoma a Filato

Abdul-raheem HassanSeptember 21, 2016

Gwamnatocin jihohin Filato da Nasarawa, sun cimma wasu matakan kawo karshen rikicin kabilu da ke lamushe rayukan al'umma shekara da shekaru.

https://p.dw.com/p/1K67s
Niger Normaden Fulani Scharfherde bei Gadabeji
Hoto: AP

Akwai alamu da ke nuna cewar zaman lafiya ya samu a tsakanin jihohin biyu, jihar Filato dai ta sha fama da tashen tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya da ke haddasa asaran rayuka a shekarun baya. To sai dai gwamnan Filato Simon Lalong yace da hawan sa mulki babban mataki daya dauka na neman sulhu tsakanin mabiya addinai da ma kabilun jihar.

Wasu daga cikin matakan zaman lafiya da mahukuntan na jihar Filato suka dauka shine kafa kommitocin sasanta jama'a daga bangaren gwamnati, da ma bangaren majalisar dokoki, inda a majalisar dokokin mataimakin kakakin majalisar Babayo Gaddi, ya shugabanci wani kommitin daya sasanta al'ummomin Fulani da Berom, da al'umomin Tarok da mazauna Kramar hukumar Wase da ma dai wasu al'umomin na Filato da suka fusknaci rigingimu a baya.

A jihar Nasarawa ma dai an sha fama da rigingimu a tsakanin 'yan kabilar Eggon da Fulani, da ma rikici Alago da Mada da kuma wasu rigingimun kabilanci da suka tabaibaye gwamnatin Tanko Almakura a shekarun baya. Amma a yanzu ana samun saukin abubuwa, Ambassada Suleiman Azores shine sakataren gwamnatin jihar Nasara a yanzu da ke ganin gwamnatin jihar ta dauki dukkanan matakan da suka wajaba da zai tabbatar da cigaban zaman lafiyar.

Mazauna wadannan jihohi biyu dai na fatan ganin tasirin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ke warewa na musamman a a ko wace shekara a matsayin ranar kiyaye zaman lafiya dan ci gaba da rungumar dabi'ar zaman lafiya a tsakanin juna, ta yadda yan baya maso tasowa zasu tarar da wasiyya mai anfani don ci gaban rayuwar su mai dorewa.