1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An taba samun ruwa mai yawa akan duniyar Mars.

Mohammad Nasiru AwalMarch 3, 2004

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amirka ta tabbatar da samun ruwa a duniyar Mars.

https://p.dw.com/p/BvlZ
Shaidar kasancewar ruwa a duniyar Mars.
Shaidar kasancewar ruwa a duniyar Mars.Hoto: AP

Tun kimanin makonni 5 da suka wuce wani karamin kumbon binciken da ake kira Mars Rover Opportunity, wanda hukumar binciken sararin samaniyar Amirka, NASA ta harba zuwa duniya Mars, ya fara aikin binciko ko shin an taba ko kuma za´a iya rayuwa a wannan duniya ta Mars. Yayin da yake magana a gun taron manema labarai, Ed Weiler daya daga cikin shugabannin hukumar ya nunar da cewa hukumar NASA tare da hadin kan kawayenta a Jamus sun tabbatar da mafarkin su.

Tun lokacin da karamin kumbon na Mars-Rover Opprtuniy ya sauka a duniya Mars kimanin makonni 5 da suka wuce yayi ta aiko da sakonni da bayyanai game da hotunan duwatsu da ke da tazarar kilomita miliyan 500 daga wannan duniya ta mu. Su kuma kwararrun masana kimiyya a hedkwatar hukumar ta NASA sun yi ta gudanar da bincike akan wadannan hotuna, kafin su bayyana sakamakon binciken na su da cewa wani abu ne mai ban al´ajabi, domin sun gano cewar duwatsun sun taba kasancewa cikin ruwa. Kumbon na Mars-Rover wanda aka yi masa tanadin kayan aiki kamar hamma da injin gina rami da kuma kyamara, ya tafiyar da aikin sa ne a matsayin wani mai binciken duwatsu. Masu binciken sun ce sun gano tarin hadadden gishiri da wasu ma´adanai a cikin duwatsu. Hakan kuwa ba ya samuwa sai da ruwa.

An dai dade ana zaton cewar da akwai ruwa a duniyar Mars, amma sai yanzu ne aka tabbatar da hakan, bayan binciken kimiyya da aka gudanar akan hotunan duwatsun dake cikin Mars. Su ma masana kimiyyar Jamus sun taka muhimmiyar rawa a binciken. Daga cikinsu kuwa akwai Gustav Klingelhofer na jami´ar birnin Mainz da kuma Ralf Gellert na cibiyar bincike ta Max-Planck-Institut.

Masu binciken sun yi imani cewar yawan ruwan da aka taba samu a duniyar ta Mars ya kai yadda za´a iya rayuwa da shi ba tare da wata mastala ba. To sai dai binciken bai tabbatar da ko an taba yin rayuwa akan duniyar ta Mars ba. Kuma duk da cewa yanzu an tabbatar da cewa an taba samun ruwa a wannan duniya to amma ba´a san ko a wani zamani ne aka samu ruwan ba. Saboda haka yanzu masana kimiyya na kokarin tura wani sabon kumbo, wanda zai iya yin jigilar duwatsu daga duniyar Mars zuwa wannan duniya ta mu, don a gudanar da bincike kai tsaye akansu. To sai dai za´a dauki shekaru da yawa kafin a cimma wannan buri.