An tantana tsakanin F W Steinmeir da Ali Larijani a game da rikicin nuklea
June 5, 2007Talla
Ministan harakokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeir, ya gana da shugaban tawagar Iran , a tantanawar rikicin makaman nuklea Ali Larjani.
Tawagogin ƙasashen 2, sun yi bitar halin da ake ciki a game da wannan badaƙala.
Kakakin ministan harakokin wajen Jamus, ya bayyana gamsuwa da tantanawar, duk da cewar ba ta cimma wani sakamakon azo a gani ba.
Ranar alhamis da ta wuce, a ka koma tebrin shawara, tsakanin Iran da ƙungiyar gamayya turai, a game da wannan rikici.
Har yanzu hukumomin Teheran, sun yi tsayuwar gwamen jaki,a game da aniyar su, ta bunƙasa makashin nuklea.