1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tara dala Billion 1.9 domin yaki da Murar tsuntsaye

Zainab A MohammadJanuary 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bu2K
Hoto: dpa

A yau ne aka kamala taron kwararru kan yaki da yaduwar kwayar cutar murar tsuntsaye a birnin Beijing din kasar Sin.

Masu bada taimako na kasa da kasa sunyi alkawarin bada tallafin kimanin dala billion 1.9 domin shawo kan annobar kwayar cutar murar tsuntsayea duniyxa baki daya,adadin daya dara abun da ake kyautata zaton cimma kashewa a kan wannan shiri.

Bankin duniya dai yayi fatan cewa kasashe zasu tara akalla dala billion guda da digo 2.

Amurka ta mayar da martini da alkawarin bayarda dala milklion 334,inda tayi Karin bayanin cewa zata bada wannan agaji ne ta hanyar kayayyakin aiki.Ayayinda kasashen dake kungiyar gamayyar turai sukayi alkawarin bayarda kusan dala million 250.

Bankin duniya ya kiyasta cewaannobar wannan cuta cikin shekara guda kachal zai iya haifar da asarar tattali a duniya baki daya na kimanin dala billion 800.

Bugu da kari milliyoyin mutane ne zasu gamu da ajalinsu idan har kwayar cutar murar tsuntsayen ta saje a jikin mutane kuma ta fara yaduwa tsakaninsu,amaimakon yanayi da ake ciki yanzu na daukar cutar daga tsuntsayen.Wanda kuma hakan zai durkusar da tattalin arzikin kasashen duniya.

Sakatare gene na mdd Kofi Annan yace tallafin da ake nema mai taka kara ya karya ban a shawo kan wannan annoba tun yanzu,idan aka kwatanta da kudin da zaa kashe idan ta mamaye duniya.

Dukkan zartarwa da zamuyi ayau shine zai taimakawa yadda zamuyi aiki tare wajen yakar wannan cuta.Bamu da sauran lokacin batawa,dole mu gaggauta mikewa tsaye.

Annan ya kara dacewa yayi amfani da tsarin mdd domin daukan matakai na ganin cewa an samu goyon baya akoda yaushe annoba ta barke.Akan hakane yayi kira ga sauran gwamnatocin kasashe dasu dauki matakai makamancin haka a kasashensu.

Ya zuwa yanzu dai cutar murar tsuntsyen ta kashe mutane 79 da bullarta a shekarata 2003,mafi ywwansu kuwa a yankin gabasghin Asia,kan gwamnatocin kasashen da wannan cuta ta bulla sunyi kira ga kasashen duniya dasu dada zage dantse wajen yakar kwayar cutar da ake kira H5N1,tare da samara da kudaden da zaa biya wadanda aka kaashe kajin kiwonsu sakamakon barkewar cutar.

A yanzu haka dai kwayar cutar ta yadu a Turkiyya ,kana sauran kasashen asia na cigaba da kasancewa da ita,inda kuma take cigaba da kashe mutane da kuma wuraren kiwon kaji da dangoginsu.

Kwararru Mahalarta wannan taron na Beijin dai sunyi gargadin cewa yaduwar wannan cuta tsakanin jammaa zai gurgunta tattalin arziki,tunda dole a killace wadanda suka kamu da ita daga gudanar da ayyukansu nay au da kullum.