1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tashi baran-baran a taron kungiyar WTO a Geneva

July 25, 2006
https://p.dw.com/p/BupH
Kwamishinan cinikaiya na KTT Peter Mandelson ya dorawa Amirka laifin janyo tsaikon da ake samu a taron kungiyar cinikaiya ta duniya WTO a game da kawad da shingayen ciniki a duniya baki daya. Mandelson yayi korafin cewa dukkan kasashe in ban da Amirka sun nuna alamun yin sassauci a tattaunawar da ake yi a birnin Geneva. Babban daraktan kungiyar WTO Pascal Lamy cewa yayi an rasa wata dama ta tarihi. Lamy ya bawa kasashe membobin kungiyar shawara da su dakatar da yarjejeniyar nan ta birnin Doha har zuwa wani lokaci da bai kayyade ba. Har yanzu dai an kasa cimma daidaito game da tallafin da ake bawa manoma musamman a kasashe masu arzikin masana´antu.