1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsare Al-Turabi

May 16, 2010

Jami'an tsaron Sudan sun kame jagoran 'yan adawan ƙasar Al'Turabi kana suka rufe jaridarsa.

https://p.dw.com/p/NPOI
Hassan TurabiHoto: AP

Mahukunta a ƙasar Sudan sun rufe jaridar jagoran 'yan adawan kasar Hassan Al-Turabi, bayan da suka yi awun gaba da shi kansa a tsakiyar daren jiya. Sakataren Al-Turabi yace a tsakiyan daren jiya jama'an tsaro cikin motoci uku suka zo suka yi awun gaba da mai gidan na sa. Kana da ranar yau suka dira a ofishin jadar Al-Turabin inda suka ƙwace ɗab'in da akayi kana suka yi awun gaba da wasu 'yan jaridu biyu da kuma babban editan jaridar. Jaridar dama jam'iyar jagoran 'yan adawanne ta PCP ke buga ta. Wannan kamun da akayiwa jagoran 'yan adawan da kuma na 'yan jaridun, ya jawo maida martane daga abokan hammaya, Inda suka yi Allah wadai da kamun da gwamnatin ta yi. Mataimakin Turabi, wato Abdallah Hassan Ahmed ya bayyana cewa za su bi duk hanyar dokar da ta kamata don ƙwato haƙƙinsu. Mahukuntan ƙasar ta Sudan, suna zargin Turabi da kalamen ɓatanci ga gwamnati da kuma fituwa a fili da ya yi na cewa zaɓen shugaba Al-Bashir da aka yi an tabka maguɗi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal