1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaurara matakan tsaro a arewacin Nigeria bayan zanga zangar zanen batanci ga Annabi MUhammad

February 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7X

Yan sanda da sojoji na cigaba da sintiri a arewacin Nigeria bayan wata zanga zanga da musulmi suka gudanar a game da zanen batanci ga Annabi Muhammad. A garin Maiduguri, jamaá da dama sun kasance a cikin gidajen su sakamakon dokar ta baci da aka kafa a jihar wanda ya biyo bayan mummunan zanga zangar da ta auku a jiya. An ruwaito cewa mutane 16 sun rasa rayukan su yayin da aka kona coci coci da Otel Otel da kuma motoci a yayin zanga zangar kafin daga bisani yan sanda su tarwatsa masu zanga zangar. Kakakin rundunar yan sandan Nigeria Haz Iwendi yace yan sanda sun kama mutane da dama a game da zanga zangar. A waje guda kuma mutum daya ya rasa ran sa a jihar Katsina a yayin wata zanga zanga domin nuna adawa da shirin gwamnatin Shugaban kasar Olusegun Obsanjo na yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar domin yin tazarce.