1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsawaita dokar hana zurga zurgar jamaá a garin Onitsa

February 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6n

Hukumomi a Nigeria sun tsawita dokar ta baci a garin Onitsa dake yankin kudu maso gabashin kasar bayan mummunan tarzoma tsakanin Christoci da musulmi da ya jawo hasarar rayukan a kalla mutane fiye da 140. kakakin gwamnatin jihar Anambara Fred Chukwulobe yace an tsawaita dokar talalar a dukkanin garuruwa da biranen jihar. Gwamnan jihar Anambara Chris Ngige ya yi umarni da a rufe makarantu. Rahotanni daga garin Enugu na cewa wasu matasan Chritoci sun afkawa musulmi domin daukar fansa ga yan uwan su da suka ce musulmi sun kashe a tarzomar da ta auku a arewacin kasar. Rigingimun sun barke ne a sakamakon zanga zangar nuna rashin amanna da zanen batanci ga manzo Annabi Muhammad, batun da ya haifar da hargitsi a kasashe da dama na duniya.