1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsawaita lokacin dokar hana fitar dare da aka kafa a birnin Bagadaza, tun ran juma’ar da ta wuce.

October 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buht

Gwamnatin Iraqi ta ba da sanarwar cewa, dokar hana fitar daren da aka kafa a birnin Bagadaza, za ta ci gaba da aiki har zuwa wani lokaci nan gaba. Sai dai ba ta ba da dalilin tsawaita wannan dokar ba. Amma wasu rahotanni na nuna cewa, wasu ’yan bindigan da ba a bayyana asalinsu ba, sun yunƙuri kutsawa cikin shiyyar nan ta tsaro a birnin, inda cibiyar gwamnati da kuma hedkwatar rundunar sojin Amirka a Iraqin suke.

A halin da ake ciki dai, ana ci gaba da samun tashe-tashen hankulla a sauran yankunan ƙasar Iraqin. A kewaye da kuma cikin garin Baquba, mai nisan kimanin kilomita 60 a arewacin Bagadaza, rahotanni sun ce mutane 8 ne suka rasa rayukansu, a cikinsu har da ’yan sanda 2, a hare-haren da ’yan tawaye suka kai a yankin. Kazalika kuma, a garin Tal Afar da ke arewacin ƙasar, a ƙalla mutane biyu ne suka sheƙa lahira, sa’annan wasu 30 kuma suka ji rauni, yayin da wani ɗan harin ƙunan baƙin wake ya ta da bam kusa da motar sintirin ’yan sanda.