1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsige gwamnan jihar Ekiti a tarayyar Najeriya.

October 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bufk

A jihar Ekiti ta tarayyar Najeriya, ’yan majalisar jihar sun tsige gwamna Ayodele Fayose da muƙaddashinsa Biodun Olujimi, a wata zaman da suka yi yau a Ado Ekiti, babban birnin jihar. Masharhanta dai na ganin matakan da aka ɗauka na tsige gwamnan, wato wata alama ce da ke nuna fafutukar da shugaba Olusegun Obasanjo na tarayyar Najeriyan ke yi, wajen mamaye iko a bainar jam’iyyrsa ta PDP wadda ke mulki a halin yanzu, kafin zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a shekarar baɗi.

Bayan tsige gwamna Fayose, sai aka naɗa spika ɗin majalisar tamkar gwamnan wucin gadi. Majalisar ta Ekiti ta ɗau wannan matakin ne makwanni kaɗan bayan da Hukumar binciken almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a, wato EFCC, wadda Obasanjo ya kafa a cikin shekara tza 2003, ta zargi gwamnonin jihohi 31 daga cikin jihohi 36 na ƙasar da almubazzaranci da cin hanci da rashawa da juya kuɗaɗen jama’a zuwa aljihunsu.

Da yake yi wa maneman labarai jawabi game da matakin tsige gwamnan jihar Ekiti da majalisar jihar ta ɗauka, shugaban hukumar ta EFCC, Nuhu Ribaɗu, ya ce ya gamsu ƙwarai da matakin. Kuma wqani kyakyawan ci gaba ne ga ƙasar ta Najeriya.

Masu sukar lamirin shugaba Obasanjo dai na zarginsa ne da yin amfani da zargin cin hanci da rashawa wajen gurgunta abokan hamayyarsa a fagen siyasa, don ya iya cin karensa babu babbaka a lokacin zaɓen da za a gudanar a shekara mai zuwa

Gwamna Fayose dai, shi ne gwamna na 3 da aka tsige a tarayyar ta Najeriya a cikin watanni 12 da suka wuce.