1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An watse baran-baram tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago da tawagar gwamnatin France

April 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2q

Bayan gagaramar, zanga zangar da ta haɗa kimanin mutane million 3, jiya a ƙasar France, an gana yau, tsakanin haɗin gwiwar ƙungiyoyin ƙwadago, da na ɗallibai, da kuma wakilan gwamnati, da na yan majalisar dokokin jam´iyar UMP, mai rinjaye, a game da batun rikicin nan ,na dokar ɗaukar sabin ma´aikata.

A sakamakon wannan tantanawa, ɓangarorin 2, sun watse baram baram, ba tare da cimma buri ba.

Ƙungiyoyin ƙwadago, sun ba gwamnati ,wa´adin 17 ga watan da mu ke ciki, domin janye kwata kwata, wannan doka, indan kuma ba haka, su ci gaba da zanga- zanga har sai , hakar su ,ta cimma ruwa.

Rikici, a kan wannan doka, ya buɗa wani saban babe, a fagen siyasar Fance, wanda ke ƙara bayyana hamayya, a fili, tsakanin Praminista, Dominique de Villepin, da ministan cikin gida, Nicolas Sarkozy, wanda a halin yanzu ,batun warware rikicin ya shiga hanun sa, a matsayin sa na shugaban jam´iyar UMP.