1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba da matakin da Majalisar Dinkin Duniya akan kasar Burma

December 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvIL

Amirka ta yabawa kuri´ar da kwamitin sulhu na MDD ya kada baya-bayan nan akan kasar Burma. Kwamitin sulhun dai ya yi kira da a yi bayanin halin siyasar wannan kasa a hukumance. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya bayyana halin da ake ciki a Burma da cewa ya tabarbare domin gwamnati a birnin Yangon na ci-gaba da tsare firsinoni siyasa kimanin dubu daya kana kuma ta tsawaita wa´adin daurin talala da take yiwa shugabar ´yan adawa Aung San Suu Khi a gida har tsawon watanni 6. A ranar alhamis da ta wuce wata kungiyar kare hakkin bil Adam a nahiyar Asiya ta ba da wani rahoto wanda a ciki ta zargi gwamnatin Burma da ganawa firsinonin siyasa azaba. A watan jiya babbar mashawartar MDD ta zartas da wani kuduri wanda a ciki ta yi tir da keta hakkin bil Adam a cikin kasar ta Burma.