1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba da sakamakon zaɓen Sabiya

January 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuTk

Ministan harkokin wajen Jamus F-W Steinmeier ya yi maraba da sakamakon zaben kasar Sabiya. A lokacin da ake fara taron ministocin harkokin waje na KTT a birnin Brussels, mista Steinmeier ya ce ko da yake masu tsattsauran ra´ayin kishin kasa suka samu rinjaye a zaben to amma masu yekuwar kafa demukiradiya zasu samu kashi 2 cikin 3 na kujerun majalisar dokokin Sabiya.

Taron na majalisar ministocin kungiyar EU zai duba yiwuwar tura wata tawagar manyan jami´ai zuwa Sabiya. Tun a cikin watan mayun bara aka dakatar da tattaunawa kara kusantar Sabiya da EU, sakamakon takaddamar da ake game da tura Sabiyawan da ake zargi da aikata laifukan yaki zuwa birnin The Hague.