1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yankewa dan adawar Masar Aiman Nur hukuncin dauri a kurkuku

December 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvFF

An yankewa dan adawar kasar Masar Aiman Nur hukuncin daurin shekaru 5 a gidan maza. An same shi da laifin shirya takardun boge lokacin da ya kafa jam´iyarsa ta Ghad ta masu sassaucin ra´ayi. An gudanar da zanga-zangar nuna adawa da wannan hukunci a ciki da kuma wajen kotun da ta yi zaman sauraron shari´a a birnin Alkahira. A cikin watan satumba Nur ya kasance babban wanda ya kalubalancin shugaba Hosni Mubarak a zaben da aka gudanar a kasar wanda kamar yadda aka sa rai shugaba Mobarak ya lashe. Don nuna adawa da tsare shi a farkon wannan wata na desamba Nur ya fara yajin kin cin abinci a gidan wakafi.