1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yankewa limamin krista hukuncin daurin shekaru 15 a Rwanda

December 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuY3

Kotun sauraron laifuffukan yaki ta mdd dake Rwanda ,zartar da hukunci kann wani Limamin krista na Roman Katholika ,adangane da samunsa da hannu a kisan kiyashin kasar da akayi a shekarata 1994.Father Athanase Seromba,na mai zama limamin Krista na farko da aka gurfanar tare da yanke masa hukunci na daurin shekaru 15 a gidan kurkuku.An samu Father Seromba dan kabilar hutu,da laifin bada umurnin rusa churchin ,inda wasu yan kabilar tutsi 2,000 suka nemi mafaka a watan Afrilun 1994,inda rusa ginin akansu yayi sanadiyyar mutuwansu baki daya.