1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi Allah wadai da hare-haren bam da aka kaiwa birnin New Delhi

October 30, 2005
https://p.dw.com/p/BvNL
MDD da kuma KTT sun yi tir da jerin hare haren da aka kai a New Delhi babban birnin kasar Indiya. Babban sakataren MDD Kofi Annan ya nuna kaduwa musamman game da cewa an kai hare hare ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da bikin ´yan Hindu na Diwali. Shi kuwa babban jami´in diplomasiyar tarayyar Turai Javier Solana cewa yayi ba wata hujjar aikata irin wannan ta´addanci akan fararen hula wadanda ba su ji ba su gani ba. Hare-haren guda 3 da aka kai kan wasu kasuwanni biyu a birnin na New Delhi sun halaka mutane fiye da 60 yayin da 200 suka jikata. Gwamnatin Indiya ta bayyana aikin da cewa na ´yan ta´adda, kuma a halin yanzu ta tsaurara matakan tsaro. Ko da yake har yanzu ba wanda ya yi ikirarin hannu a hare-haren amma an kame mutane 10 da ake zargin cewa suna da wata masaniya game da wannan aika-aika.