1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi batakashi tsakanin magoya bayan Hamas da Fatah

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv12

´Yan bindiga na kungiyar Hamas dake jan ragamar mulki da aboklan gabarsu na kungiyar Fatah sun yi musayar wuta da jefa nakiyoyi da bama-bamai akan juna a wani artabu da suka yi yau a birnin Gaza. Hakan ta faru ne kwana daya kacal bayan da shugaban bangaren siyasa na Hamas Khaled Mashaal ya zargi shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da cin amanar al´umar Falasdinu. Akalla mutane 15 sun samu raunuka a arangamar da aka yi. Magoya bayan Fatah sun kwashe ranary au asabar sun a gudanar da zanga-zanga akan tituna don yin tir da kalaman na Mashaal. Da farko sun fara jifar juna da duwatsu sannan daga bisani wasu ´yan bindiga daga bangarorin Hamas da fatah suka fara budewa juna wuta.