1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi belin Ingrid Betankurt

Mayr, Jakob / Buenos Aires (BR) July 3, 2008

Sojojin Kolombiya sun ƙwato Ingrid Betankurt daga hannun ´yan tawayen FARC

https://p.dw.com/p/EVGn
Ingrid Betancourt ta kubuta da hannun ´yan tawayen FARCHoto: AP



Bayan shekaru shida da tayi tsare  cikin hannuwan´yan tawayen FARC,a jiya sojojin Kolombiya sun yi nasara ceton  Ingrid Betankurt, bafarasansa kuma yar takara a zaɓen shugaban ƙasar  Kolumbiya.

Wakilin DW a birnin Bogota na ƙasar Kolombiya Jalob Mayar ya aiko da rahoto, wanda Yahouza Sadissou Madobi ya fasasara ,mana.


Ingrid Betankurt ta sauko daga jirgi, a filin saukar jiragen sama na Bogota sanye da hulla da ƙaramar riga,da  baƙin wando da kuma dogayen takalma masu rufe ƙafa. Ta sauko ta na mulmushi, kuma  da alamun ta na cikin koshin lafiya.

Ma´aifiyarta da mijinta, na jiran ta a filin jirgin wanda saukarta ke da wuya ta yi masu gasuwa ta mussamman, ta kuma yi bayani kamar haka:Ina godiya ga dukkan mutanen ƙasar Kolumbiya, ina godiya ga jama´ar duniya baki ɗaya, da suka tashi tsayin daka, don kaiwa ga wannan nasara.

Ina godiya ga shugaban ƙasa da kuma sojoji.

Ingrid Betankurt ta ci gaba da bayyana yadda sojojin suka same ta suka kuma bayyana mata wannan albishir mai daɗi:shugaban rundunar ne ya same mu, ya sanar da mu cewar mu sojojin gwamnati ne, daga yanzu kun fita daga matsayin pirsinoni, abun kamar dai cikin mafarki, daga nan sai ya rungume mu yana gaida mu, bamu yi zatan da gaske bane.

Da muka fahinci dai da gaske ne, sai nace da shi gaskiya kayi mana babbar kyauta, wadda za mu taɓa mantawa da ita ba.

Bayan Ingrid Betankurt, sojojin gwamnatin Kolombiya sun ceto Amurikawa ukku da kuma sojojkin gwamnati 11 da yan tawayenFARC suka yi garkuwa da su.

Wasu daga cikinsu suns hare shekaru fiye da goma a cikin hannun ´yan tawayen. Dukkan su sun yi farin ciki tare da godiya ga shugaba Alvaro Uribe na Kolombiya.

An samu belin firsinonin bayan fafatawar da aka gwabza, tsakanin dakarun FARC da na gwamnatin a kurmin Kolombiya dake tazara kilomita 400 da Bagota babban birnin kasar.

Wannan nasara da sojojin gwamnati suka samu, ta ƙara ƙarfin gwiwa ga al´umar Kolombiya a game da yaƙi da ´yan tawaye , a cewar ministan tsaron ƙasar, Juan Manuel Santos, dakaru za su cigaba  da kutsawa har sai sun gama kwata kwata da ƙungiyar FARC: babu shaka wannan nasara ce a gare mu, amma ba za mu tsaya anan ba, za mu bayanawa jama´a ƙarin haske zuwa gaba.

Shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy da yayi ruwa yayi tsaki wajen ceton rayuwar Ingrid Betankurt  ya hurta albarkacin bakinsa a game da wannan nasara:Da sunana da sunan ministan harakokin waje Bernard Kouchner, muna issar da sahihiyar godiya da shugaban ƙasa Alvaro Uribe da gwamnatinsa, da kuma sojojin Kolombiya da suka cimma wannan gagaramar nasara.

Baƙi ɗaya France ta yi godiya ta ƙara.

A halin da ake ciki dai ƙasashe dabam dabam na duniya na cigaba da  murna tare da jinjina damtse ga ƙasar Kolombiya.

A yayin da yake nasa jawabi shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez da ya zama mai shiga tsakani  a wannan rikici yayi kira ga ´yan tawayen FARC su yi belin sauran firsinonin dake cikin hanunsu.