1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi bikin rattaba hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kungiyar EU a birnin Rom

Mohammad Nasiru AwalOctober 29, 2004
https://p.dw.com/p/Bvf1
Shugabannin EU a wajen bikin rattaba hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kungiyar
Shugabannin EU a wajen bikin rattaba hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kungiyarHoto: AP

Huskokin dukkan shugabannin da suka hallara a Rom babban birnin kasar Italiya na cike da annashuwa, musamman dangane da bikin sanya hannu akan sabon kundin tsarin mulkin KTT EU. A cikin sa´o´i kalilan an manta da rashin jituwar da aka samu dangane da wakilan sabuwar hukumar zartaswar kungiyar karkashin sabon shugabanta Mista Barroso. A karon farko wannan kundin tsarin mulkin zai kasance wata doka ta bai daya ga dukkan al´umomin kasashen kungiyar EU, wanda kuma har wala yau zai karfafa ikon siyasar kasashen Turai.

A lokacin da yake yiwa shugabannin kasashe da na gwamnatocin kungiyar EU marhabin mai karbar baki kuma FM Italiya Silvio Berlusconi ya kira wannan rana da cewa wata rana ce ta musamman.

O-Ton Berlusconi: Das heutige Tag...

"Samun damar halartar wannan biki a yau wani muhimmin abu ne na tarihi."

FM Berlusconni yayi tuni da cewa a wannan zaure da aka sanya hannu akan sabon kundin tsarin kungiyar ta EU a nan ne kimanin shekaru 47 da suka wuce aka yi bikin rattaba hannu kan yarjeniyoyin birnin Rom, wadanda suka share fagen kirkiro kungiyar tarayyar Turai. FM na Italiya ya bayyana bikin na yau da cewa wani muhimmin mataki ne da nahiyar Turai ta dauka, wanda a wancan lokaci ba wanda ya yi tsammanin zata kai ga haka.

O-Ton Berlusconi: Noch nie in der....

"Babu wani lokaci a cikin tarihi da dokokin demukiradiyya da walwala suka taka wata rawa mai muhimmanci da ya kai a wannan marra da muke ciki, inda aka samar da wata doka ta bai daya ga miliyoyin jama´a."

Gwamnatin Italiya da hukumar birnin Rom sun kashe kudi kimanin Euro miliyan 10 a shirye-shiryen gudanar da bikin. Yayin da aka kashe Euro miliyan 4 wajen kawata gine-ginen dake kusa da zauren da aka yi bikin.

An dai yi bikin cin abincin rana bayan an sanya hannu kann kundin tsarin mulkin, hakazalika bisa ga dukkan alamu ba wanda ya tuna da rashin jituwar da aka samu a wannan mako dangane da sabuwar hukumar zartaswar kungiyar EU. Hatta shi kanshi sabon shugaban hukumar mai jiran gado mista Barroso ya halarci bikin na birnin Rom, inda ya tattauna da sauran shugabannin kungiyar EU don samun mafita wajen nada sabbin wakilan hukumar kungiyar ta EU, wadanda zasu samu amincewar majalisar dokokin Turai.