1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi garkuwa da mutane a Philippin

Gazali Abdou Tasawa
June 21, 2017

Mayakan Kungiyar Biff ta masu da'awar jihadi a Philippin sun kutsa a cikin wata makarantar firamare  ta birnin Pigkanawayan a wannan Laraba inda suka yi garkuwa da tarin farararen hula. 

https://p.dw.com/p/2f7Cb
Philippinen Islamistische Rebellengruppe BIFF
Hoto: Getty Images/AFP/T. Aljibe

Rahotanni daga kasar Philippin na cewa wasu mayakan kungiyar Biff ta masu da'awar jihadi sun kutsa a cikin wata makarantar firamare  ta birnin Pigkanawayan a wannan Laraba inda suka yi garkuwa da tarin farararen hula. 

Tun da sanyin safiyar ne dai mayakan 'yan jihadi kimanin 100 suka kai farmaki kan wata cibiyar sojojin kasar kafin daga bisani wasu kimanin 30 daga cikinsu su kutsa a cikin makarantar inda suka yi garkuwa da mutanen da ke ciki tare kuma da jan daga. 

Birnin na Pigkawayan na a nisan kilomita 160 da birnin Marawawi na tsibirin Mindanao wanda mafiyawancin al'ummarsa Kiristoci ne.

Sama da wata dayakenan yankin yake fuskantar jerin hare-haren masu kaifin kishin Islama da ke da'awar yin mubayi'a ga Kungiyar IS.