1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi garkuwa da wasu mutane kusan 50 a Iraq

March 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5X

Rahotanni daga gabashin kasar Iraqi sun nunar da cewa wasu yan bindiga dadi sunyi garkuwa da wasu ma´aikata kusan 50, dake aiki a wani kamfani mai zaman kansa.

Yan bindiga dadin dake sanye da kayan yan sanda sun sanya mutanen ne a cikin wasu motoci kusan goma da suka je ma´aikatar dasu.

Kafin dai faruwar hakan sai da dakarun sojin Amurka suka gano gawarwakin mutane 18 a cikin wata mota kirar bus a yammacin Birnin Bagadaza.

A cewar jami´an tsaron kasar dukkannin matattun na sanye ne da ankwa a hannayen su, kuma da alama sai da aka gallaza musu kafin kashe su.