An yi garkuwa da wasu turawa yan yawan shaƙatawa a gabacin ƙasar Niger
August 22, 2006Talla
Sanarwa daga Opishin ministan harakokin wajen ƙasar italia, ta bayana cewar wasu mutane ɗauke da makamai sun yi awan gaba, da yan yawan shaƙatawa fiye da 20, a gabacin Jamhuriya Niger gap ga iyaka da Tchad.
Al´ammarin ya wakana a yammacin jiya.
Daga cikin turawan da a ka kama, 21 yan ƙasar Italia ne.
Sanarwar ta ce, wani ɗan yawan shaƙatawa [Y1] na ƙasar Jamus, da ya ƙetara rijiya da baya, ya bada wannan labari.
Ya zuwa yanzu, babu labari a hukunce, daga Niger ko kuma Tchad, da ya bada ƙarin haske a game da batun.
Ƙaramin opishin jikadancin Italia dake ƙasar Cote d´Ivoire ya tura tawaga ta mussamman a Jamhuriya Niger, domin samin ƙarin haske.
Sannan Italia, ta shiga tantanawa da opisoshin jikadancin Jamus da na France, da ke birnin Niamey.