1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a kara yawan sojojin Amirka a Iraki da Afghanistan

December 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuXq

Hafsan sojin kasa na Amirka Janar Peter Schoomaker ya yi kira da a kara yawan dakarun kasar a kasashen Iraqi da Afghanistan. A lokacin da yake magana a gaban wani kwamitin kwararru na majalisar dokoki a birnin Washington janar din ya ce idan ba´a yi haka ba to ba za´a iya gudanar da aikin da aka sa a gaba ba. Janar din ya nuna bukatar karin yawan sojoji dubu 6 zuwa dubu 7 a kowace shekara. A kuma can Iraqi an sako day awa daga cikin mutanen da wasu ´yan bindiga dadi suka sace jiya a tsakiyar birnin Bagadaza.