1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a kara yawan sojojin NATO a kudancin Afghanistan

September 8, 2006
https://p.dw.com/p/BukG
Manyan shugabanni biyu na kungiyar tsaro ta NATO sun yi kira ga kasashe membobin kungiyar da su ba da karin dakaru ga yakin da ake yi da sojojin sa kai na Taliban a kudancin Afghanistan. A wani taron manema labarai da yayi a garin Mons na Belgium, Hafsan sojin Amirka, Janar James Jones wanda shi ne babban kwamandan kula da aikin soji na NATO, yayi kira da a ba da karin sojoji akalla dubu 2. shi kuwa sakatare janar na NATO ya fadawa manema labari ne a birnin Brussels cewa dole ne membobin kungiyar kawancen su taimaka dakarun Birtaniya da Kanada da NL dake jagorantar gumurzun da ake yi da ´yan tsageru a kudancin Afghanistan. Jami´an diplomasiya a birnin na Brussels sun ce Jamus wadda ke jagorantar tawagar NATO a arewacin Afghanistan, inda ake da dan kwanciyar hankali, tana shan matsin lamba na ta ba da gudunmmawar sojoji ga kudancin kasar ta Afghanistan. To amma kakakin ma´aikatar tsaron Jamus ya ce kasar ba zata ba da kai ga wannan matsin lambar ba.