1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a kare mata daga fyade da suke fuskanta a Darfur

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYg
Wasu shahararrun mata sun yi kira ga gamaiayar kasa da kasa da ta kara daukar matakan kare mata daga ayyukan fyade da suke fuskanta kullu yaumin a yankin Darfur mai fama da rikici dake yammacin Sudan. A cikin budaddiyar wasika da aka buga yau jajebiren ranar duniya ta Darfur, matan suka ce a kullum ana amfani da yiwa mata fyade da cin zarafin su a matsayin wani makami na yakin na Darfur. Daga cikin wadanda suka sanya hannu kan wasikar akwai tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amirka Madeleine Albright da kwamishinar kare hakkin bil Adama ta MDD Mary Robinson da tsohuwar Firaministar Faransa Edith Cresson. A kuma halin da ake ciki FM Birtaniya Tony Blair ya yi roko ga gwamnatin Sudan da da ´yan tawaye da su aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya nan take kana kuma su fara neman hanyoyin warware rikici cikin lumana.