1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira da a tattauna da ´yan Islama na ƙasar Somalia

January 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuVA

Mai kula da manufofin gwamnatin Amirka a kan nahiyar Afirka, Jendayi Frazer ta tattauna yau da kakakin majalisar dokokin Somalia a birnin Nairobi. Frazer ta gana da Sherif Hasan Sheikh Aden wanda gwamnatin wucin gadin Somalia ke zargi da cin amana saboda alakarsa da ´yan Islama na kasar. An yi ganawar ne bayan da Frazer ta soke wata ziyarar da ta yi shirin kaiwa birnin Mogadishu saboda dalilai na rashin tsaro. Frazer ta goyi da bayan tattuanwa da wasu daga cikin ´yan Islama tana mai cewa.

“Ina ganin yana da muhimmanci mun tattauna da masu sassaucin ra´ayin na kawancen kotunan Islama saboda lalle suna da kwarewa kuma sun maido da bin doka da oda a birnin Mogadishu.”

Aden wanda kusa ne a fagen siyasar Somalia, ya rasa goyon bayan daga gwamnatin wucin gadi wadda ta zarge shi da kokarin yin sulhu da ´yan Islama ba tare da izinin ta ba.