1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira ga shugabannin Afirka da su mayar da hankali a rikicin Darfur da Somalia

July 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bus1
Shugaban kungiyar tarayyar Afirka AU Alpha Omar Konare yayi kira ga shugabannin kasashen Afirka da su kara mayar da himma a kokarin warware rikicin yankin Darfur dake kasar Sudan da kuma mawuyacin halin da ake ciki a kasar Somalia. A lokacin da yake jawabin bude taron kolin kungiyar AU a birnin Banjul na kasar Gambia shugaba Konare ya ce dole a yi duk abin ya wajaba don aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a watan mayu tsakanin gwamnatin Sudan da ´yan tawayen lardin Darfur. Shi kuma a nasa bangaren babban sakataren MDD Kofi Annan cewa yayi halin da ake ciki a Darfur na daya daga cikin munana na wannan marra da muke ciki. Ko da yake muhimmin batun dake kann ajandar taron shi ne na hadin kann tattalin arzikin kasashe 52 membobin kungiyar ta AU, amma rikicin Darfur da halin da ake ciki a Somalia sun daukar hankalin mahalarta taron.