1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi kira ga ´yan Iraƙi da su sasanta

December 2, 2007
https://p.dw.com/p/CVpQ
A dangane da kyautatuwar harkokin tsaro, Amirka ta yi kira ga ´yan Iraqi da su fara wani taron yin sulhu tsakanin ´yan ƙasar. A ƙarshen ziyarar kwanaki shida da ya kai Iraqi, mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amirka John Negroponte ya ce yanzu lokaci yayi da ya kamata a ƙarfafa nasarar da ake samu wajen tabbatar da tsaron cikin gida. Tun bayan da Amirka ta kara yawan dakarun ta da sojoji dubu 30 aka samu raguwar tashe tashen hankula a Iraqi. A kuma halin da ake ciki jam´iyar kawance ta Islama wadda ke zaman wata kungiyar ´yan Sunni mafi girma a Iraƙi, ta ba da sanarwar kawo ƙarshen ƙauracewa zaman majalisar dokoki da ta ke yi.