1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi maraba da sakin wakilin BBC Alan Johnston a Zirin Gaza

July 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuH6

Kasashen duniya sun yi maraba da sakin wakilin BBC a Zirin Gaza Alan Jonhston. Babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana ya ce yayi matukar murna da sako Johnston. Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas yayi maraba da sakin wakilin na BBC bayan ya shafe makonni 16 a hannun wasu ´yan takifen Falasdinawa. Shi ma ministan harkokin wajen Jamus F.-W. Steimeier ya nuna jin dadinsa game da sakin Johnston mai shekaru 45 a duniya. Ita ma Faransa ta yi maraba da haka. Shi kuwa shugaban Hamas dake gudun hijira Khaled Mashal ya ce nasarar da aka samu a tattaunawar da aka yi dangane da makomar Johnston, wata shaida ce cewar kungiyar Hamas ka iya maido da bin doka da oda a Zirin Gaza. Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa game da wannan ci-gaba da aka samu Mustafa Bargutti dan majalisar dokokin Falasdinawa ya janyo hankalin duniya ne game da halin da al´umar Falasdinu ke ciki.