1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi suka ga shirin tinkarar sauyin yanayi na G8

Awal, MohammadJuly 9, 2008

Ƙasashen China da Indiya sun ƙi buƙatar G8 na rage yawan hayaƙi mai ɗumama doron ƙasa.

https://p.dw.com/p/EYyz
Shugabannin G8 na dasa itatuwa a JapanHoto: AP

Ƙasashen China da Indiya sun ce ba su da niyar sanya hannu kan wani shirin rage yawan gurɓataccen hayaƙin da suke fitarwa kamar yadda ƙasashen da suka fi ci-gaban masana´antu suka amince da nufin rage yawan wannan hayaƙi da kashi 50 cikin100 kafin shekara ta 2050.


Ƙasashe masu ci gaban da masana´antu da ƙasashen da ke kan gaba wajen samun bunƙasar tattalin arziki a yanzu sun kasa samun fahimtar juna game da wani takamammen buri ko lokacin dangane da rage yawan hayaƙin da ke haddasa ɗumamar yanayi. Ko da yake a ƙarshen taron ƙolin na haɗin guiwa a tsibirin Toyako da ke ƙasar Japan ƙasashen 16 sun bayyana alhakin da ke kansu amma sun kasa cimma matsaya ta bai ɗaya kan wani ƙuduri a yaƙin da ake yi da ɗumamar doron ƙasa.


Kamar yadda tawagogin ƙasashe daga zauren taron suka nunar ƙasashe kamar su China da Indiya sun ce ba su da niyar amincewa da wani shirin rage fid da iskar carbon dioxide mai ɗumama yanayi da misalin kashi 50 cikin 100 kafin shekara ta 2050 kamar yadda manyan ƙasashen duniya mafiya ƙarfin tattalin arziki suka amince a jiya Talata. To amma wani jami´i a fadar shugaban ƙasar Faransa ya faɗawa manema labaru cewa ƙasashen China da Indiya da suka fi samun bunƙasar tattalin arziki a nahiyar Asiya, waɗanda kuma a jimilce dukansu biyu ke fid da kashi 25 cikin 100 na hayaƙin da masana kimiya suka ce shi ke ɗumama doron ƙasa, sun ce suna da niyar ɗaukar mataki nan gaba. Jami´in ya nunar da haka ne bayan wani taron haɗin guiwa tsakanin ƙungiyar G8 da China, Indiya, Afirka Ta Kudu, Mexico da Brazil inda suka tattauna game da sauyin yanayi.


Ko da yake manazarta al´amuran yau da kullum sun yi suka game da rashin ɗaukar ƙawararan matakai bisa manufa amma an jiyo shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta na yabawa da ƙudurin da G8 ta ɗauka tana mai cewa.

"A dangane da batun yanayi muna iya cewa an samu gagarumin ci-gaba idan aka kwatanta da taron Heiligendamm. A bana mun samu daidaito akan abbubuwan da suka hana ruwa gudu a bara. "


Shi ma shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barraso ya tofa albarkacin bakinsa ya na mai cewa.


" Wannan wani ci-gaba ne amma ba 100 bisa 100 ba. Domin har yanzu ba a amince gaba ɗaya game da burin da aka sanya a gaba ba."


A ƙarshe dai dukkan ƙasashen masu arzikin masana´antu da masu tasowa sun amince cewa sauyin yanayi na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalolin dake gaban duniya a wannan lokaci.