1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi sulhu tsakanin yan FNL ga gwamnatin Burundi

June 19, 2006
https://p.dw.com/p/ButH

Gwamnatin Burundi, da yan tawayen FNL, sun rataba hannu a kan yarjejeniyar samar da zaman lahia ,a wannan ƙasa, da ke fama da yaƙe-yaƙe a tsawan shekaru 13.

An rataba hannu kan yajejeniyar a birnin Dar-es Salam na ƙasar Tanzania.

Mahimman ƙudurorin da ta ƙunsa, sun tanadi cewar, ɓangarorin 2, sun amince su tsagaita wuta, sannan su ci gaba da tantanawa, domin samar da zaman lahia na dindidin, nan da sati 2 masu zuwa.

Bayan cimma wannan mataki, ƙungiyar tawayen FNL za ta rikiɗa zuwa jama´iyar siyasa.

Gwamnati ta yi alƙawarin afuwa ga dukan yan tawayen, da zaran yarjejeniyar ta fara aiki, kuma take, za a fara belin pirsinonin yaƙi na ɓangarorin 2.

Ya zuwa yanzu, babban batun da a ke kai ruwa rana kansa, shine na rundunar tsaro ta ƙasa.

Yan tawayen na buƙatar ayi mata garambawul, a yayin da gwamnati, ta ce hakan ba zata saɓu ba.

Tawagogin 2, za su sake haɗuwa ranar yau litinin domin cigaba da tantanawa.