1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi tir da ganuwar da Amirka zata gina kan iyakar ta da Mexico

October 27, 2006
https://p.dw.com/p/BueH
Shugaban Mexico mai jiran gado Felipe Calderon ya yi suka da kakkausar harshe akan shirin Amirka na gina wata doguwar katanga akan iyakar kasashen biyu. A wata ziyarar da yake kaiwa Canada, mista Caldeton ya kwatanta katangar da bangon Berlin. A jiya shugaban Amirka GWB ya sanya hannu kan dokar da ta amince da gina katangar mai tsawon kilomita dubu daya da 100. Katangar wadda za´a gina ta don dakile kwararar bakin haure daga Mexico zuwa Amirka, zata kunshi waya masu kayoyi da kyamerori masu iya daukar hoto cikin duhu da na´urorin hangen nesa. A kowace shekara dubun dubatan bakin haure daga Mexico na tsallake iyakar ta barauniyar hanya suna shiga Amirka.