1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi tir da harin kunar bakin wake na birnin Bagadaza

April 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2g
Tashe-Tashen hankula a Abidjan
Tashe-Tashen hankula a AbidjanHoto: AP

Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi Allah wadai da harin bam din da aka kai jiya akan wani masallacin ´yan shi´a a birnin Bagadaza wanda ya halaka mutane 79. Annan ya ce manufar maharan shine su haddasa gaba tsakanin al´umomin Iraqi. Harin wanda aka kai akan masallacin Buratha dake birnin Bagadaza shi ne mafi muni cikin watanni 3 kuma wasu ´yan kunar bakin wake su uku su kai harin. Biyu daga cikin su sun yi shiga ce ta mata. Harin ya kuma raunata akalla mutane 150. Jakadan Amirka a Bagadaza yayi gargadin game da barkewar wani yakin basasa tsakanin ´yan shi´a da ´yan sunni, idan kokarin da ake yi na kafa gwamnati ya ci-tura. A dai halin da ake ciki ´yan siyasa na bangaren Sunni da kurdawa sun ki yi aiki da FM rikon kwarya Ibrahim E-Jaafari, wanda yayi watsi da kira da suka yi masa da yayi murabus.