1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi zanga-zangar yin Allah wadai da Amirka a Mogadishu

June 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buvc

Dubun dubatan mutane sun gudanar da zanga-zanga a Mogadishu babban birnin kasar Somalia don nuna adawa da taimakon da Amirka ke baya wani kawance da ya yi shailar yaki da ta´addanci. Masu zanga-zangar, wasunsu dauke da bindigogin Kalashnikov, sun yi ta rera wakokin yin Allah wadai da Amirka tare da yin harbi a cikin iska. An shafe makonni da dama ana dauki ba dadi a birnin Mogadishu tsakanin musulmi sojojin sa kai da wani kawancen madugan yaki da wakilan ministocin gwamnatin rikon kwarya da Amirka ke marawa baya. Akalla mutane 300 aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka wakana a wurare da dama na Mogadishu.