1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi zanga-zangar yin tir da shirin tsimin kudi na gwamnatin Jamus

October 21, 2006
https://p.dw.com/p/Buf4

Sama da mutane dubu 200 sun gudanar da zanga-zanga a manyan biranen Jamus guda biyar don nuna adawa da shirin tsuke bakin aljihun gwamnati. Babbar kungiyar kwadago ta tarayyar Jamus ta shirya zanga-zanga, inda aka yi gangami mafi girma a birnin Stuttgart. ´Yan kwadago na zargin gwamnatin kawance karkashin jagorancin shugabar gwamnati Angela Merkel da tafyiar da wata manufa da zata gurgunta tsarin tallafawa marasa galihu a cikin kasar. To sai Merkel ta kare wannan manufa a wani jawabi da ta yiwa taron matasa na jam´iyar ta CDU a birnin Wiesbaden. Ta ce karin haraji da za´a yi a farkon shekara mai zuwa zai taimaka talakawan kasar su samu karin kudi a cikin aljihunsu.