1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi Jawad al-Maliki a mukamin sabon Firaministan Iraki

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv11

Majalisar dokokin Iraki ta sake zaban shugaba Jalal Talabani don yin wani sabon wa´adi na shekaru 4. Yanzu haka dai Talabani wanda Bakurde ne ya dorawa Jawad al-Maliki wanda dan shi´a ne nauyin kafa sabuwar gwamnati. Maliki dai shi ne na biyu a mukami a cikin jam´iyar Dawa ta tsohon FM Ibrahim al-Jaafari. Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yaba da nadin al-Maliki da cewa muhimmin mataki ne da zai ka ga kafa dawwammamiyar gwamnati a Iraqi bayan an shafe watanni 4 ana fama da kiki-kaka na siyasa. Sabon FM ya ce zai goyi da bayan shigar da sojoji sa kai na jam´iyun adawa cikin rundunar sojin kasar. Da farko majalisar dokoki ta zabi dan sunni Mahmud al-Majhadani a matsayin shugabanta. An kawo karshen takun saka tsakanin al´umomin kasar game da kafa sabuwar gwamnati bayan da tsohon FM al-Jaafari ya amince da janye takarar sake neman wannan mukami.