1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi ƙungiyar al-Qaida da hannu a kisan da aka yiwa Bhutto

December 29, 2007
https://p.dw.com/p/Chim
Hukumomin ƙasar Pakistan sun zargi wata ƙungiyar masu tsattsauran ra´ayin Islama dake da alaƙa da ƙungiyar al-Qaida da hannu a kisan da aka yiwa tsohuwar Firaministan ƙasar Benazir Bhutto. Kamar yadda ma´aikatar cikin gida a birnin Islamabad ta nunar, hukumomin leƙen asiri sun samu wannan labari ne daga mayaƙan wani jagoran ƙungiyar al-´Qaida a Pakistan. To sai dai jam´iyar Bhutto ta yi watsi da wannan labari dake cewa jagoran sojojin sa kai wato Mehsud ke da hannu a wannan kisan gilla da aka yiwa tsouwar Firaministan mai shekaru 54 a duniya. A halin da ake ciki jami´an tsaro na ci-gaba da sintiri a kokarin kwantar da tarzoma da magoya bayanta suka tayar. Yanzu haka dai mutane 27 suka rasa rayukansu sakamakon wannan tarzoma. A jiya jumaa aka yi jana´izar Bhutto a mahaifarta dake lardin Sindh na kudancin Pakistan.