1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi Amurka da mutuwar fursunoni a Guantanamo

June 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuuQ

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar Saudiya,sun dora laifin mutuwar yan kasar 2 da a kace sun kashe kansu a gidan fursunan Guantamo akan kasar Amurka,yayinda ake rade radin cewa dakarun sojin Amurkan sun azabtar da wadannan fursunoni ne har suka rasa rayukansu daga bisani suka ce sun rataye kawunasu ne.

Mutuwar fursunonin na saudiya 2 ya taba ruhin dangantakar dake tsakanin Amurka da Saudiya.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar sun bukaci a gudanar da bincike game da musabbabin mutuwar tasu.

Lauyan yan uwan wadanda suka rasun Kateb al Shimri,yace yanuwan nasu basu yarda cewa wadannan mutane zasu kashe kansu ba,kamar yadda sauran jamaar saudin suma suka dauka,saboda haka yace ya shirya kaiwa karar gwamnatin Amurka domin ta biya diyya ga yan uwan mamatan.

Yanzu haka dai,kakain gwamnatin saudiya Mansour Turki yace gwamnati tuni ta fara shirye shiryen kawo gawarwakin yan kasar tata 2 da suka rasa rayukansu.