1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi gwamnatin Sudan ci-gaba da kai farmaki kan ´yan Darfur

September 12, 2006
https://p.dw.com/p/Buju

Babban sakataren MDD Kofi Annan ya zargi gwamnatin Sudan da karya dokokin yarjejeniyar samar da zaman lafiya a lardin Darfur dake fama da rikici. A cikin wani jawabi da ya yiwa kwamitin Sulhu Annan ya ce ana kai sabbin hare hare ta sama yayin da ake ci-gaba da gwabza kazamin fada a yankin na Darfur. Mista Annan ya kuma yi zargin cewa ana hana kungiyoyin ba da agaji tafiyar da aikin su. A kuma halin da ake ciki da yawa daga cikin membobin kwamitin sulhu sun yi kira ga mahukuntan birnin Khartoum da su janye adawar da suke nunawa shirin girke dakarun MDD a lardin na Darfur. A ganawar da ta yi da ministan harkokin wajen Sudan Lam Akol a birnin Washington sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce dangataka tsakanin kasashen biyu zata ingantu ne idan gwamnatin Sudan ta amince da girke dakarun na MDD.