1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi gwamnatin Tunisia da laifin azbtar da fursinonin siyasa--

July 8, 2004

Kungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Tnisia da laifin tsare fursinonin siyasa tsawon lokaci--

https://p.dw.com/p/BviJ
Ministan cikin gidan Jamus a lokacin da ya kai ziyarar aiki kasar Tunisia.
Ministan cikin gidan Jamus a lokacin da ya kai ziyarar aiki kasar Tunisia.Hoto: AP

Kungiyar kare hakin bil adama ta human Rights Watch ta zargi gwamnatin kasar Tunisia da laifin tsare fursinonin siyasa a gidajen yari na kasar ba bisa ka’ida ba har na tsawon shekaru 13 ba tare da an sako su ba.

Kungiyar kare hakin bil adaman dai ta kasa da kasa ta baiyana cewar kasar ta Tunisia dake arewacin Africa,kann tsare fursinonin kimanin 40 a dan karamin dakin tsare masu laifi,da bai dace a ce an tsare masu laifin tsawon lokaci ba,wanda kuma yin hakan ya sabawa tsarin dokoki na kasa da kasa.A mafi yawan lokaci dai akan tsare fursinoni a dan karamin dakin tsare masu laifi har na tsawon sa’oi 23 koma fiye da haka,ba kuma tare an samar da issasun tagogin da isska zata rika ratsawa ta ciki ba.

Cikin wani rahoto mai shafuka 33 da kungiyar kare hakin bil adama ta human Rights mai mazuni a birnin Paris ta fitar,ta baiyana cewar lokaci kalin ake baiwa iyalan masu laifin su ziyarce su a gidan kurku,yayin kuma da aka haramtawa fursinonin siyasar na kasar Tunisia damar jin wani labari daga kowace kafar yadda labari ko kuma karanta litatafai.

A sabili da haka ne sarah Leah Whitson daractar kungiyar kare hakin bil adama ta kasa da kasa dake lura da yakin gabas ta tsakiya da arewacin Africa,baiyana damuwarta kann irin matakan da gwamnatin Tunisia ke dauka na nuna rashin imani ga fursinonin siyasar da ake tsare da su,inda hakan ke nuni da cewar an tauye hakin fursinonin siyasa a kasar ta Tunisia.

Yawanci fursinonin siyasar da gwamnatin kasar Tunisia ke tsare da su yayan jama’iyar musulunci ta Nahdha da aka haramtawa gudanar da harkokin su na siyasa a wanan kasa ta arewacin Africa.

Kasar dai ta Tunisia ta baiyana cewar jama’iyar ta masu kishin Islama ta Nahdah,jama’iya ce ta kungiyoyin tsagerun musulmi masu zazafan ra’ayi na addini,wanda kuma ke kokarin kifar da gwamnati su kafa ta su ta masu tsatsaran ra’ayin addini.

A shekara ta 1992 wasu kotuna na soji a kasar ta Tunisia sun zartar da hukunci kann mutane 265 da ake zargin nada hanun cikin shirya makarkashiyar kifar da gwamnati.

Kungiyoyin kare hakin bil adama na duniya sun zargin cewar ba’a gudanar da adalci wajen zartar da hukunci kann mutanen da ake zargin sun yi yunkurin kifar da gwamnati ba.

Babu daya daga cikin wadanda ake yiwa wanan zargi da aka kama da laifin gudanar da aiyuka irin na yan tarzoma ba.

Har kawo yanzu dai gwamnatin kasar Tunisia bata mayar da martani kann bukatun da kungiyoyin kare hakin bil adama ta human Rights Watch ta gabatar ba na a bawa jami’anta damar ziyartar gidajajen yarin kasar ta Tunisia.

Kungiyar dai ta kare hakin bil adama ta kasa da kasa ta sami yin hira da iyalan wanda ake tsare da su din,inda kuma suka sami cikakun bayanai game da muyacin hali da gidajen kurkukun kasar Tunisia ke ciki a halin yanzu.