1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi gwamnatoci da nuna halin ko-in-kula ga bala´o´i da suka addabi duniya

October 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvOu
Kungiyar ba da agaji ta Birtaniya wato Oxfam ta yi zargin cewa gwamnatoci na tafiyar hawainiya tare da nuna halin ko-in-kula wajen tinkarar bala´o´i irin daban-daban a fadin duniya baki daya. A cikin wani rahoto da ta bayar a birnin London kungiyar ta Oxfam ta ce a lokuta dama ana danganta ba da taimakon jin kai ga akidoji na siyasa ko kuma irin muhimmancin da kafofin yada labaru suka ba wa abin maimakon a mayar da hankali wajen duba bukatun mutanen da ke a yankunan da bala´i ya afkawa. Kungiyar ta ce sabanin yawan taimakon da aka bayar bayan aukuwar bala´in igiyar ruwan Tsunami a cikin watan desamban bara da kuma mummunar girgizar kasar da ta auku a Pakisan a cikin wannan wata, sau tari akan yi tsimi wajen ba da taimako ga yankunan da ke fama da rikici amma ba sa shiga kanun labarai kamar Darfur, Nijer ko JDK.