1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ɗaukar kananan yara aikin soji a Kongo

December 14, 2007
https://p.dw.com/p/Cbtb
Ana ci-gaba da tilastawa ƙananan yara shiga aikin soji a yakin basasan da ake yi a gabashin Janhuriyar Demokuraɗiyya Kongo. Kamar yadda tawagar MƊD a Kongo ta nunar a cikin watanni shidda da suka wuce an samun karuwar yawan ƙananan yara da ake shigar su cikin yakin musamman a arewacin lardin Kivu. Kakakin MƊD ya yi kira ga sojoji da kuma madugun ´yan tawaye janar Laurent Nkunda da su kwance ɗamarun sojojin ƙananan yara. A cikin makonnin bayan nan fada ya kara yin muni a yankin, inda aka tilastawa mutane kimanin dubu 400 tserewa daga yankin tun a farkon wannan shekara.