Ana bukatar jerin sauye sauye cikin kungiyar EU
December 18, 2005Talla
Shugaba Jacques Chirac na Faransa ya ba da sanarwar cewa za´a aiwatar da jerin sauye-sauye masu alfanu a cikin KTT EU. A lokacin da ya ke magana a birnin Paris, shugaba Chirac ya ce hukumomin kungiyar EU a yanzu ba su dace da sabon yanayi na fadada Turai da kuma sabunta ta ba. Shugaban ya ce burin su yanzu shi ne a mayar da nahiyar Turai ta zamo mai taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya baki daya. A jiya asabar ne shugabannin tarayyar Turai suka amince da yarjejeniya akan kasafin kudin kungiyar EU na shekaru 7 a wani mataki na hana kungiyar fadawa cikin wani mummunan rikicin kudi. Dukkan shugabannin kungiyar sun yi maraba da yarjejeniyar.