1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da ƙazamar fafatawa tsakanin dakarun Isra’ila da mayaƙan ƙungiyar Hizbullahi.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupP

A yankin Gabas Ta Tsakiya, har ila yau ana ta ci gaba da ba ta kashi tsakanin dakarun Isra’ila da mayaƙan ƙungiyar Hizbullahi. Yayin da Isra’ilan ke ta hadarin bamabamai da jiragen saman yaƙinta a birnin Beirut da kuma yankunan gabashi da kudancin Lebanon, ’yan ƙungiyar Hizbullahi kuma na ci gaba da harba rokokinsu zuwa birnin tashar jirgin ruwa na Haifa. Kawo yanzu dai, sama da mutane dari 3 da 60 ne suka rasa rayukansu a Lebanon, sakamakon farmakin da Isra’ila ke kai wa ƙasar. A ɓangaren Isra’ila kuma, mutane 37 ne suka rasa rayukansu kawo yanzu. Rahotanni dai sun ce, Isra’ilan na ci gaba da tara dakarunta a kan iyakarta da Lebanon, abin da ke alamta cewa tana niyyar yin wani gagarumin ɗaukin soji ne a ƙasar.

Tuni dai, Siriya ta yi barazanar cewa, ita ma za ta shiga yaƙin, idan dakarun Isra’ilan suka kutsa cikin Lebanon suka kuma doshi iyakarta. Ministan yaɗa labaran ƙasar, Moshen Bilal ne ya bayyana haka, a cikin watta fira da ya yi da jariadar ABC ta ƙasar Spain.