1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da babban taron nahiyar Afirka a Bonn

November 6, 2005
https://p.dw.com/p/BvMP

A yau lahadi za´a ci-gaba da babban taron yini biyu game da nahiyar Afirka a Petersberg dake nan birnin Bonn don tattauna sabbbin hanyoyin da za´a bi don inganta manufofin raya kasashe masu tasowa. Taron mai taken Kawance da Afirka, wani sabon shiri ne na shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler da nufin ba kasashen nahiyar Afirka damar fada a ji a manufofin raya kasashe matalauta. In an jima da rana, shugaba Köhler hade da shugaban ATK Thabo Mbeki da takwaransa na Nijeriya Olusegun Obasanjo da FM Habasha Meles Zenawi zasu shiga cikin tattaunawar. Taron zai kuma tattauna akan huldar dangantaku tsakanin Jamus da kasashen Afirka.