1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da bijirewa Sarki Gyanendra na Nepal

April 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv18

Duk da sanarwar da sarki Gynendrah na Nepal ,ya bayar na dawowa da mulkin demukiradiya cikin kasar, har yanzu ana ci-gaba da zanga-zangar bijire masa. Dubun dubatan mutane a a babban birnin kasar da ma wasu birane sun sake yin zanga-zangar nuna adawa da matakan takaita mulkin da sarkin ya dauka. Bayan an shafe makonni da dama ana gudanar da zanga-zanga a wasu wuraren ma har da zubar da jini, a jiya Basaraken ya ba da sanarwar yin sassauci ga matsayin na tafiyar da tsarin mulki irin na mulukiya. Sarki Gyanendrah ya yi kira ga kawancen jam´iyun adawa su 7 da su ba da sunan wanda ya fi cancanta a bashi mukamin FM. Yayin da yake magana a birnin New York babban sakataren MDD Kofi Annan yayi fatan cewa wannan sassauci da Basaraken ya nuna zai maido da mulkin demukiradiya a kasar nan ba da dadewa ba. A kuma halin da ake ciki gwamnatin Nepal ta kafa dokar hana fita ta sa´o´i 8 a kowace rana a birnin Kathmandu. Wata sanarwar gwamnati ta ce dokar zata yi aiki a babban birnin da unguwar Lalipur dake wajen birnin.