1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da dambarwar siyasa a Hungary

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buil

Daruruwan ´yan sanda a Budapest babban birnin Hungary sun yi feshi ruwa da harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zanga dake neman FM Ferenc Gyurcsany da yayi murabus. To amma FM ya ce ba zai mika kai ga bukatun masu zanga-zangar ba ya na mai cewa gwamnatinsa zata ci-gaba da aiwatar da shirin ta na canje canje. Masu zanga-zangar sun cunnawa motocin ´yan sanda da dama wuta tare da jifar jami´an tsaron da sanyin safiyar yau laraba rana ta biyu a tarzomar da ake yi bayan da FM ya amasa cewar gwamnatinsa ta yi ta yiwa jama´a karya game da matsayin tattalin arzikin kasar. ´Yan sanda kimanin 140 da masu zanga-zanga da dama suka jikata a tashe tashen hankulan. A kuma halin da ake ciki shugaban ´yan adawa Viktor Orban ya ce zaben kananan hukumomi da za´a gudanar a kasar a ranar daya ga watan oktoba zai zama tamkar kuri´ar raba gardama ga gwamnatin dake ci.