1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci-gaba da fafatawa tsakanin dakarun Libanon da ´ya´yan Fatah al-Islam

May 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuL1
Kwana na biyu a jere dakarun Lebanon na ci-gaba da musayar wuta da sojojin sa kai a wani sansanin ´yan gudun hijirar Falasdinawa sdake arewacin Libanon. Wadanda suka shaida abin da ke faruwa sun ce akalla fararen hula 7 aka kashe yayin da fiye da mutum 70 suka jikata a fadan na yau. A fafatawar da aka yi jiya lahadi a wannan sansanin an halaka akalla mutane 50 tare da jiya 90 rauni. Sansanin inda ´yan gudun hijirar Falasdinawa kimanin dubu 40 suka samu mafaka, ya kasance cibiyar kungiyar Fatah al-Islam ta masu tsattsauran ra´ayi. A halin da ake ciki majalisar ministocin Libanon ta zargi kungiyar da kokarin haddasa rudami a cikin kasar a daidai lokacin da MDD ke shirin kafa wata kotun kasa da kasa wadda zata yi shari´ar mutanen da ake zargi da hannu a kisan da aka yiwa tsohon FM Libanon Rafik Hariri a shekara ta 2005.